Obasanjo yace bai san shekarun sa nawa ba a Duniya
Yayin da ake shirin bikin cika shekara 80 a Duniya na tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo, ya kuma fito ya ba Jama’a mamaki inda yace kai bai ma san ko shekarun sa nawa ba.
Jiya ne tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bai san ko asalin shekarun sa nawa ba. Obasanjo yace shi dai abin da mahaifiyar sa ta fada masa shi ne an haife sa a ranar cin kasuwa.
Obasanjo yace bai san takamammen ranar da aka haife sa ba domin iyayen sa ba su iya rubutu da karatu ba. Obasanjo yace mahaifiyar sa ta shirya tafiya kasuwa ne kurum sai nakuda ya kama ta, a haka ne dai aka haifi tsohon shugaban kasar.
KU KARANTA: An nadawa Osinbajo sarauta
Obasanjo ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da yara inda ya rika raba masu kyautar littatafai a Garin sa da ke Abeokuta. Obasanjo yace kawai dai ya kiyasta ranar haihuwar ne ko da yake ba na asali bane, amma kusan lokacin da aka haife sa kenan.
A jiya kuma aka yi wa mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo nadin sarauta a Garin Akwa-Ibom. Farfesa Yemi Osinbajo ya zama ‘Obong Emem’ na Garin Akwa Ibom.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng