An kama wani don ya zagi Buhari?

An kama wani don ya zagi Buhari?

– Hukumar DSS ta damke wani babban Dan adawar shugaba Buhari a Legas

– Gbadamosi ya maka Hukumar kara a Kotu

– An dai rasa laifin da wannan mutumi yayi

An kama wani don ya zagi Buhari?
An kama wani don ya zagi Buhari?

Hukumar ‘Yan sanda na farar kaya watau DSS sun damke wani dan PDP kuma dan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun garkame na kwana da kwanaki. Yanzu dai Ggadamosi Tunde ya shigar da kara a babban kotun kasar da ke Legas.

Mista Ggadamosi Tunde wanda jigo ne na Jam’iyyar PDP ta Jihar Legas ya kuma kasance babban ‘Dan adawar shugaba Muhammadu Buhari har a kafafen zamani. Sai dai ba a san laifin da wannan mutumi yayi har ta kai aka damke sa ba.

KU KARANTA: An kama wani dan ta'addan Duniya a Najeriya

Tuni dai Mista Ggadamosi ya maka Hukumar ta DSS kara a Kotu saboda garkame sa da aka yin a dogon lokaci ba tare da an maka sa a Kotu ba. Tun kwanakin baya dai Jami’an DSS suka kama Tunde Ggadamosi suka kuma wuce da shi Garin Abuja wanda har yanzu babu wanda ya san meke faruwa.

Wannan makon kuma Femi Falana SAN, Lauyan shugaban kungiyar IMN Ibrahim Az-Zakzaky, ya rubuta wasika ga Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo SAN da kuma Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami SAN game da cigaba da daure malamin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng