Wasu nau'ikan abinci 5 da bai kamata ka ci ba da dare

Wasu nau'ikan abinci 5 da bai kamata ka ci ba da dare

- Akwai wasu nau`ikan abinci da bai kamata a ci ba a wasu lokuta

- Wasu mutanen kan shiga bandaki fiye da kima yayin da su ka ci abincin da ke sa fitsari musamman ma da daddare.

Wasu nau'ikan abinci 5 da bai kamata ka ci ba da dare
Wasu nau'ikan abinci 5 da bai kamata ka ci ba da dare

Bisa al`ada mutane kan ci abinci da safe da rana da kuma dare, amma babu wani binciken kimiyya da ya tilasta karara cewa sau uku kadai za a ci abinci daga fitowar rana zuwa faduwarta.

Abin da yawancin masana a fannin abinci su ka hadu a kai shi ne, in dai mutum ba azumi ya ke ba, to ya kamata ya karya kumallo da wuri.

Mafi jinkiri karfe 9:00 zuwa 10:00 na safe, yayin da za a ci abincin rana tsakanin karfe 12:00 zuwa 2:00 na a tsakar rana.

Shi kuwa abincin dare ya fi dacewa a ci shi kamar karfe 7:00 na yamma ko kuma karfe 8:00 a jinkirce.

Dalilin haka kuwa shi ne, akwai wasu nau`ikan abinci da in aka ci su da yawa da daddare za su hana mutum jin dadin barci, za su sa cushewar ciki ko kuma yawan fitsari.

Wasu daga cikin wadannan nau`ikan abincin sun hada da:

1. Sakwara

Sakwara wani gama garin abinci ne a jihohin Ekiti da Ondo da Osun kai har a tsakanin Kabilun Inyamurai da wasu Hausawa ma su na sonta. Sai dai wata matsala ta cin Sakwara in dare ya yi shi ne cushewar ciki, ta na kuma sa kasala da barci. Ya fi kyau a ci ta da rana.

Wasu nau'ikan abinci 5 da bai kamata ka ci ba da dare
Abinci irin su Tuwo da sakwara bai kamata a ci su da dare ba

2. Amala

Yarabawa na cin Amala sosai. Ana yin ta garin busasshiyar doya. Amala na samuwa ne yayin da aka tuka garin doya da ruwan zafi a tukunya. Tana daya daga abincin da ke sa yawan yin fitsari in aka ci da daddare. Duk da cewa tana narkewa da wuri, tana haifar da yawan fitsari sosai.

3. Mummuki (burodi)

Burodi na daya daga cikin nau`ikan abincin da aka fi ci a Najeriya. Dalibai da masu sana`ar hannu ne su ka ci. Shi ke bin bayan shinkafa, abincin da `yan Najeriya su ka fi amfani da shi. Shi ma cinsa da daddare na cushe ciki.

4. Wake

Wake iri-iri ne. Amma a kudanci a kan ci shi tare da Burodi, wanda hakan ke haifar da yawan shan ruwa. In dai aka ci wake da daddare, to shi ma yana cushe ciki saboda kasancewarsa nau'in protein.

5. Koko

Ana yin sa da masara. Ya fi kyau a sha shi da safe. Duk da cewa musulmai na yawan amfani da shi lokacin azumi wajen shan ruwa, da yawa mutane na shan sa da safe. Yarabawa na kiransa Ogi da Hausa ana ce masa koko yayin da Iinyamurai ke kiransa Akamu.

A ci dadi lafiya: Ga wani hoton bidiyo kan farfesun naman akuya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng