Abubuwa 11 game da kudurin dokar karin aure ta jihar Kano
Ga wasu abubuwa 11 dangane da kudurin dokar kayyade aure da Sarkin Kano ya ke kokarin aiwatarwa a jihar Kano domin yiwa mata gata a cewarsa.
A wata hira da Sarkin Kano ya yi da wata 'yar jarida a jihar, Sarkin ya bayyana wasu muhimman abubuwa da kuddurin dokar da masarautar Kano ta ke son gani ta aiwatar domin yiwa mata gata a jihar kamar haka:
I. Aure da ma'anarsa
Dokar ta yi magana a kan aure. Menene aure kuma iri nawa ne wanne ne mai kyau wannene batacce.
2. 'yancin zabar miji
Ta tabbatar wa da 'ya mace baliga 'yancin ta zabi mijinta kuma ta haramta ayi wa ya baligha auren dole ba izninta.
3. Karamar yarinya
Bi sa sharadi idan za a aurar da karamar yarinya sosai to sai an je an karbi iznin alkalin shari'a wanda zai yi shawara da likitoci kuma ya tabbatar da maslahar yarinyar ce kuma larura ne ba za a iya jira ba kafin ya zartar. Saboda a tabbatar shekarunta ya kamata tana makaranta kuma duk wani tsinkaye ya nuna hadarin juna-biyu a wajen karamar yarinya.
4. Dukan Mace
Sannan wannan doka ta haramta dukan mace kuma wanda ya yiwa matarsa rauni akwai qisaasi ko diyya kamar yadda shari'a ta tanada.
5. Tabbatar da hakkin ciyarwa da shayarwa
Dokar ta tabbatar da hakkin ciyarwa da tufatarwa da mahalli da lafiya kuma idan mutum na da hali yaki yi to alkali zai umurce shi yayi. Idan ya ki alkali na da ikon ya kwaci dukiyarsa a ciyar da iyalinsa. Idan ma ya hana har daure shi sai a yi kamar mai bashi.
6. Auren mace fiye da daya
Wanda zai auri mace fiye da daya akwai sharudda a cikin littattafan mazhaba wadanda ba a la'akari da su an fito da su an sa a dokar. Saboda haka wanda ba zai iya kula da hakkin mace ba ba zai aureta ba sai dai idan ita tana da halinta kuma tace ta dauke masa nafaqa.
7. Zama gida daya
Haka ba zai hada su makwanci daya ko wajen zama ko girki daya ba sai idan su sun yarda su zauna haka duk wannan shari'a ce tabbatacciya a cikin littattafai.
8. Kyautatawa mace
Akwai kyautatawa mace da dukiya idan an sake ta. Akwai hakkin kula da duk dan da aka haifa.
9. Tazarar Haihuwa
Akwai maganar halaccin tazara tsakanin yara da amfani da hanyar jinkirta haihuwa wacce ba ta sabawa shari'ar addinin musulunci ba.
10. Gado
Akwai maganar ahliyya da wasiyya da gado da sauransu . Babban kundine sosai. An gama kashi na farko wajen tsara dokar da za a kai gaban babban kwamiti nan ba da dadewa ba. Idan sun yi gyara ko tabbatar da shi daga nan za a rubuta shi da sigar dokar mu nemi majalisa da tayi doka sannan mu bukaci mai girma Gwamna yasa hannu.
11. Hujjoji da daga Qur'ani da Hadisi
Ana kiyayewa mata darajarsu ne domin su iyayen al'umma ne. Maganar wanda ba zai iya rike mata ba kada yayi aure ba sabuwa bace. Allah ya fada a cikin al qur'ani
وليستعفف الذين لا يجدون نكاحاً حتى يغنيهم الله من فضله
Ma'ana wadanda ba su da halin aure su kame kansu har sai Allah ya wadatar da su daga cikin falalarsa. Saboda haka Allah ya hana wanda ba shi da halin kula da mace ya yi aure kuma shi ne abinda ake tabbatarwa a kasashen musulunci da yawa. Haka manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce
ايها الشباب. من استطاع الباعة منكم فليتزوج. فان لم يستطع فعليه بالصوم.
Ma'ana ya ku samari wanda yake da halin aure a cikin ku yayi aure. Wanda ba shi da hali ya yi azumi.
Asali: Legit.ng