Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa

Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa

– Wani Saurayi ya auri wanda ta yi jika da shi

– An dai ce ita soyayya ba ruwan ta

– Dan shekara 28 ya auri tsohuwa ‘yar 82

Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa
Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa

Da yake shi ‘so’ ba gani yake yi ba, ga dai wani matashi na dan shekara 28 ya buge da auren wanda ta girme sa da shekaru 54 a Duniya. Wannan abu dai ya faru ne a can kasar Indonesia.

Ko da yake dangin juna ba su so wannan aure ba amma aikin gama ya gama tun da masoyan suka ce sun ji sun gani. Kwanan baya ne wani matashi mai aikin kwadago Sofian Laho Dandel ya shiga soyayya da wata tsohuwa Martha mai shekaru fiye da 80 a Indonesia.

KU KARANTA: Matsalar Arewacin Najeriya-Sarkin Kano

Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa
Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa

Kamar yadda jaridar Tribune news ta kawo tace yanzu har an shirya aure duk da banbancin shekarun. Martha dai tsohuwa ce wanda ta rasa mijin ta shekaru fiye da 10 da suka wuce, ta kuma ce yanzu ita da Sofian, mutu ka raba; takalmin kaza.

Bisa dukkanin alamu dai Duniyar nan ta zo karshe don kuwa kwanaki muka samu wani labari da ba mu taba jin irin sa ba shi ma. A Kasar Zambia wani saurayi ne ya auri mahaifiyar sa bayan uban sa ya rasu.

Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa
Rikici ko soyayya: Wani ya auri kakar sa

A same mu a http://twitter.com/naijcomhausa ko kuma https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel