Kana da labarin abin da zai faru Ranar Lahadi a Najeriya?

Kana da labarin abin da zai faru Ranar Lahadi a Najeriya?

– Za a samu husufin rana a Najeriya

– Masu nazari sun ce Ranar Lahadi wannan abu zai faru

– Sai dai an ce abin ba zai yi kamari ba

Kana da labarin abin da zai faru Ranar Lahadi a Najeriya?
Wata zai kama rana a Najeriya

Masana masu hange da binciken Duniya sun bayyana cewa za a samu husufin rana a sassan kasar nan a Ranar Lahadi. Ko da yake dai masanan sun ce abin ba wani mai kamarin gaske bane.

Kungiyar bincike game da cigaban sararai na kasa watau NASRDA tace wannan abu zai faru ne karshen makon nan kamar yadda ta fadawa hukumar dillacin labarai na kasa NAN jiya a Birnin Abuja.

KU KARANTA: Meyasa talauci yayi yawa a Arewa?

Masanan sun ce wannan abu zai faru ne a ko ina na fadin kasar. Hasken ranar za ta fi raguwa ne kuma a Yankin kudancin kasar irin su Fatakwal, Kalaba da Garin Uyo. Inda kuma abin ba zai yi wani tasiri ba shi ne Yankin Arewacin kasar musamman Jihar Kebbi.

Wannan abu dai zai faru ne da yammaci akasari daga bayan karfe 4 zuwa karfe 6. Ba dai yau aka fara samun husufi a Najeriya ba, kuma ba abin tada hankali bane. A irin wannan yanayi mutane kan fito suyi ta addu’a.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng