Matashiya mai shekara 18 ta yasar da jariri a karkashin gada saboda ta kasa gane Uban yaron

Matashiya mai shekara 18 ta yasar da jariri a karkashin gada saboda ta kasa gane Uban yaron

Wata uwa mai shekaru 18 da tayi yunkurin yasar da jaririnta a karkashin gadar Oshodi, ta yi bayanin abunda ya kai ta ga yanke wannan mummunan shawarar.

Matashiya mai shekara 18 ta yasar da jariri a karkashin gada saboda ta kasa gane Uban yaron

An kama wata matashiya mai shekaru 18 da ta bayyana sunanta a matsayin Timilehin Adeshina kwanan nan a lokacin da take yunkurin yasar da jaririn ta dan watanni 4 a duniya a karkashin gadar Oshodi a jihar Lagas.

An saka jaririn a cikin wani jaka tsirara, sannan uwar tasa ta yasar da shi, wacce daga bisani wasu jami’an hukumar tsaro na jihar Lagas suka kama ta.

KU KARANTA KUMA: Anga dodanni suna siyan kankara a kan titi (HOTUNA)

Da take bayanin dalilin ta na yasar da yaron, Timilehin wacce ta bar makaranta a aji biyu na sakandare, tace:

“Mahaifiya ta kore ni saboda na kasa sanin mutumin da yayi mun ciki. Nayi jima’I da mazaje daban-daban.”

Ta kuma bayyana cewa tana bacci da mazaje daban daban wadanda ke bata kudi, don kawai ta samu na al’amuran yau da kullun, tunda mahaifinta yam utu shekaru tara da suka wuce.

Tuni dai an mika Timilehin ga sashin kula da jin dadin matasa da ci gabansu na jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng