Shema ya musanta tuhumar sata akansa, kotu ta bada belinsa akan naira biliyan daya

Shema ya musanta tuhumar sata akansa, kotu ta bada belinsa akan naira biliyan daya

Tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema ya musanta tuhume tuhumen zargin sata da ake yi masa har guda 22, tare da wasu mutane guda uku.

Shema ya musanta tuhumar sata akansa, kotu ta bada belinsa akan naira biliyan daya
Shema

Hukumar EFCC ta gurfanar da Shehu Shema ne a gaban babban kotun jihar Katsina, wanda Alkali Maikaita Bako ke jagoranta tare da wasu munate guda uku da suka hada da tsohon babban sakatari a ma’aikatar kananan hukumomi Rufai Safana, tsohon kwamishinan kananan hukumomin Sani Makana da tsohon shugaban ALGON Lawal Dankaba kan zargin wadaka tare da karkatar da kudaden al’umma kusan naira biliyan 11.

KU KARANTA: Sakataren gwamnati Babachir ba miciyin amanar Buhari bane’ – inji wata Ƙungiya

Da fari dai sai da kotun ta tabbatar da cewar tana da hurumin sauraron karar ba kamar yadda lauyan Shema yayi ikirari ba tun a baya, inda yace ministan shari’a nada daman gurfanar da kowane irin mai laifi a kowane kotun kasar nan.

Sa’anan Alkalin ya kara da cewa EFCC a matsayinta na hukumar gwamnatin tarayya nada daman gurfanar da duk wani dake tuhuma da laifin almundahanr kudi gaba kowane irin kotun kasar nan, amma bayan dogon muhawara da murza gashin baki ne sai alkalin ya bada belinsu akan naira biliyan daya duk mutum daya tare da wakili guda guda.

Daga karshe kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng