Kungiyar musulman Shi’a sunyi sihiri a kan Buhari (HOTUNA)
Kungiyar musulman Shi’a, wadanda suka samu sabani da gwamnatin Najeriya, tayi wani sihiri a jiya, Lahadi, 19 ga watan Fabrairu, a jihar Borno kan lafiyar shugaban kasa Buhari.
A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, Khalid Abdul, anyi sihirin ne don shugaban kasar Najeriya, Buhari wanda ke hutun ganin likita a birnin Landan, ya mutu a chan. A cewar rahotanni, mutanen basa farin ciki da gwamnati saboda ci gaba da tsare masu shugaban su Ibrahim El Zakzaky da gwamnatin keyi.
Kungiyar ta yanka shanu sannan ta zuba jinin shanun a cikin wani rami sannan suka kewaye ramin suka kuma cinna wuta.
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta soke bikin zagayowar ranar haihuwarta
Kalli karin hotuna a kasa:
Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng