HOTO: Atiku, IBB na cikin ganawa

HOTO: Atiku, IBB na cikin ganawa

An saki wani hoton game da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a lokacin ganawa da tsohon shugaban kasa mulkin soja, Ibrahim Badamosi Babangida (IBB)

HOTO: Atiku, IBB na cikin ganawa
HOTO: Atiku, IBB na cikin ganawa

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ganawar ta biyo bayan ziyarar da Atiku ya kai wa IBB a gidansa dake Hilltop Minna, babban birnin jihar Niger a ranar Talata, 14 ga watan Fabrairu.

Ana ta rade-radin cewa Atiku Abubakar, wanda ya zauna matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Obasanjo, na da kudirin tsayawa takarar zabe a 2019.

Yayinda ba’a san cikakken abunda taron tsakanin mutanen biyu ya kunsa ba, wasu masana harkan siyasa sun ce taron na iya nasaba da rade-radin kudin Atiku na tsayawa takarar shugabanci a 2019.

Ku tuna cewa a watan Nuwamba 2016 wata kungiya mai suna Coalition Democracy ta yarda da tsayawar Atiku Abubakar takarar shugabanci a 2019 kan cewa dan siyasan dana abunda ya cancanta don kara inganta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel