‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa

‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa

– Dan wasan Liverpool ya sha da kyar

– ‘Yan iskan gari sun kai wa dan wasan Liverpool Sadio Mane hari

– Dan wasa Mane ya zubar da finariti ne Gasar kwallon Nahiyar Afrika

‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa
‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa

Wasu tsagera sun kai hari gidan wani dan wasan Liverpool saboda jin haushin ya zubar da finariti a Gasar cin kofin nahiyar Afrika. Dan wasa Mane ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a karawar kasar sa ta Sanagal da Kamaru.

Kasar Sanagal dai ta sha kashi ne a hannun Kamaru da ci 5- 4, kuma dan wasa Sadio Mane ne ya barar da na sa bugun wanda ta sa aka koro kasar gida. Kasar Kamaru dai ce ta samu lashe gasar nahiyar watau AFCON.

KU KARANTA: Wata ta nuna ba ta son Dan wasa Ronaldo na Madrid

‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa
‘Yan iskan gari sun nemi su hallaka wani babban dan wasa

Zafin hakan ne ya sa aka kai wa dan wasan hari har gidan dangin su da ke Unguwar Malika a Ingila. Duk da dai ba a kashe kowa ba, amma ‘yan iskan garin sun yi barna inda suka lalata wata katuwar motar ‘jif’ da dan wasan. Yanzu haka dai maganar ta na wurin ‘Yan Sanda inji Jaridar The Sun.

A Ingilar dai mun samu labari cewa Kungiyar Manchester United ta Ingila ta kafa tarihin da ba a taba samu ba a Kasar Ingila. Man Utd tana da maki 2000 wanda tun da aka fara Gasar zuwa yanzu, a Duniyar kwallon Ingilar dai ba a taba kai wannan mataki ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel