Ko ka taba ganin ‘Yar autar Buhari?
– Ko ka taba ganin Diyar shugaba Muhammadu Buhari Hannan
– Hannan ita ce ‘yar autar Baba Buhari
– Hannan Buhari tana sha’awar daukar hotuna
Wasu hotunan diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayyana a shafin gizo. An dai ga ‘yar autar shugaban kasan a wani hoto rike da ‘kemera’ abin daukar hoto. Hannan din dai tana da sha’awar daukar hotuna.
Hannan Muhammadu Buhari ta dauro hoton ne a shafin ta a cikin bakin launi. Sai dai masu bin Diyar shugaban kasar a yanar gizo sun tofa albarkacin bakin su a game da hoton. Jama’a dai suna cewa Diyar shugaban kasar tana da dan-karen kyau.
KU KARANTA: An gano Biliyoyin kudi na sata a Najeriya
Sai dai wani daga cikin masu-bin Diyar shugaban kasar ya ba ta shawarar cewa bai dace ta saka bakin hoto ba, watau kamar ana wani makoki. Ana dai ta rade-radin cewa shugaba Buhari na kwance a Landan bai da lafiya.
Kwanan nan ne kuma dai aka ga wani hoton Zahra Buhari da Angon ta Ahmed Indimi suna cigaba da soyewa abin su bayan daurin auren su. An ga Zahra Buhari ta dafa kan Sahibin na ta inda shi kuma ya fito da harshen sa waje.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng