Kallo ya koma sama: Magidanci ya maka matarsa a kotu don tana jibgarsa

Kallo ya koma sama: Magidanci ya maka matarsa a kotu don tana jibgarsa

Wani magidanci Mista Kasimu Oseni ya kai karar matarsa gaban kotun gargajiya dake garin Lugbe a babban birnin tarayya Abuja, inda ya bukaci kotun ta tsinka igiyar aurensa da matarsa Rebecca saboda yawan jibgarsa da take yi kamar Allah ya aiko ta.

Kallo ya koma sama: Magidanci ya maka matarsa a kotu don tana jibgarsa
Turnuku

Oseni ya koka kan yarda uwargidarsa wanda suka yi auren soyayya ta mayar da shi tamkar ganga abin duka, inda yace da zarar ya dan yi mata ba daidai ba, sai ta zage karfinta tayi ta makar sa.

“A gaskiya ina yin iya kokarina wajen ganin na biya mata dukkanin bukatunta, amma sai na lura ita kam yar rikici ce kuma tana yawan son fada. Gaskiya ni ba haka na san ake rayuwar aure ba, don haka ban tunani zan iya cigaba da rayuwa ta a haka.” Inji Oseni.

KU KARANTA: Anyi wata ganawar sirri tsakanin Osinbajo da manyan hafsoshin tsaro

Oseni ya shaida ma kotu cewar yayansu biyu da Rebecca, inda ya kara da cewa shi kadai tilo yake daukan dawainiyar matar da yayan nasu guda 2, musamman biyan kudaden makaranta.

Oseni ya fada ma kotu “don haka ina rokon kotu ta bani ikon dauke yarana, saboda zamansu dani shine maslahar su, idan ba haka ba Rebecca zata lahanta su.”

Sai dai Oseni ya kara da cewa dama ai Rebecca tana da yara hudu daga aurenta na farko, kuma baya da yawan duka, bata amsa kiransa a duk lokacin daya bukace ta, a takaice dai Mista Oseni yace ya gaji da zaman nasu.

Sai dai uwargida Rebecca ta musanta duka zarge zargen da Oseni yayi mata, hakan ya sanya alkali mai shari’a Esther Omavuezi yanke hukuncin neman karin shaidu da hujjoji daga bangarorin guda biyu.

Sa’annan alkalin ta dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Feburairu, duk da haka ta shawarce su dasu yi amfani da kwanakin dake tsakani don sulhunta kansu kafin a cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng