Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef

Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta sayi wani yaron dan kwallo da asalin kasar Najeriya mai shekaru 13, Lateef Omidji.

Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef

Rahotannin sun bayyana cewar, manyan masu horar da yan kwallo da suka hada da Wenger, Conte Klopp ne suka yi ribibin siyan dan wasa Lateef daga kungiyar Sparta Rotterdam sakamakon nuna bajinta da yayi a kungiyar.

KU KARANTA: Sarkin Zazzau ya nemi gafaran al'ummar masarautar Zariya

Bugu da kari rahoton yace suma Barcelona da Real Madrid sun sanya idanu akan dan wasan, sai dai Arsene Wenger yayi musu zafin nama wajen saye yaron ba tare da wata wata ba.

Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef
Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef

“Aresenal ta lura da alamun kwarewar dan wasan, don haka ne suka yanke shawarar siyan sa don sake gina shi yadda ya kamata, Lateef zai dinga yin atisaye a kungiyar Arsenal, kuma kocawansa zasu dinga binsa kasar Hollanda don lura da shi.” Inji rahoton.

Cinikin dare? Arsenal ta sayi wani dan wasan Najeriya, Abdul Lateef

Sai dai a yanzu akwai sauran aiki a gaban Lateef, domin kuwa ana bukatar sa daya jajirce sosai a shekaru hudu masu zuwa kafin Arsenal ta bashi daman rattafa hannu.

Ga bidiyon Lateef Omidji nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng