Buhari ya fatattaki Sojoji daga Villa
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Sojojin da ke masa gadi
– Da alamu dai an samu baraka ne ta hannun Sojojin
– Kamar yadda aka saba Jami’an DSS za su cigaba da kare shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari duk ta kare ya salami Sojojin da ke gadin sa ya kuma maye gurbin su da Jami’an DSS kamar dai yadda aka saba a baya. Ba mamaki an samu matsala ne ta wajen Sojojin da ke gadin na sa.
Jaridar The Nations tace daf da shugaba Buhari zai tafi Landan ya bada wannan umarnin ya nemi Sojojin da ke gadin sa su bar fadar shugaban kasar. Asali dama can Jami’an DSS ne ke aikin kare shugaban kasa da iyalan sa.
KU KARANTA: Makafi sun yi zanga-zanga
Farkon hawan shugaban kasa Buhari ya kori Jami’an DSS da ke gadin shugaban kasa ya dauko Sojoji a matsayin su. Hakan dai ya kawo matsala tsakanin dogarin shugaban kasar Kanal Abubakar Lawal da kuma shugaban masu kare sa Abdulrahman Mani. Har daga karshe dai shugaba Buhari ya sallami Mani daga aiki, sai dai yanzu kamar an koma gidan jiyar.
Gwamnatin tarrayar Najeriya ta dai fito yayi magana game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lai Mohammed ya musanya rade-radin da Jama’a ke ta yadawa a kasa game da shugaban, yace Buhari na nan garau.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng