Wata mata ta roƙi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda yawan duka

Wata mata ta roƙi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda yawan duka

Wata tela a garin Ibadan Uwargida Omotolani Alele ta roki wata kotun gargajiya dake Agodi, jihar Ibadan a ranar Laraba 8 ga watan Feburairu data tsinka igiyar aure dake tsakaninta da mijinta, wanda tace bashi da aiki sai jibgarta kawai don bata yarda ta bauta ma gumaka, kamar yadda shi mijin yake yi.

Wata mata ta roƙi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda yawan duka

Ita dai Omotolani wadda take zaune a unguwar Ojoo na garin Ibadan ta kai kara kotun ne don ta raba aurenta sakamakon cin mutunci, duka da tsangwama da mijin ta mai suna Anthony ke nuna mata.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewar tun a ranar 1 ga watan Feburairu ne kotu ta fara sauraron karar, daga nan ta dage shi zuwa ranar 8 ga watan Feburairu, don baiwa mijin damar kawo takardar shaidan aurensu bayan matar tayi ikirarin cewar ba’a daura musu aure a kan ka’ida ba, sai dai a ranar sake sauraron karar, sai wanda ake kara ya gagara kawo takardar shaidan daurin auren.

KU KARANTA: Wataƙila Buhari yawo dawo gida Najeriya ranar Asabar

Yayin da take jawabi ga kotu, Uwargida Omotolani tace dansu daya mai shekaru 3, amma tayi matukar da-na-sanin zama da Anthony saboda cin mutunci dayake yi mata.

“Mijina yana yawan bukata da in dinga bauta ma gunkin dangin su, amma naki yarda nayi, hakan ya sanya shi dukana a kullum.

“Da fari ma iyayensa basa son zaman mu, amma dai muka nace saboda yace yana so na, amam komai ya canza yanzu. Har ma ya dauke danmu, kuma bansan inda ya kai shi ba. Don haka nake rokon kotu data raba auren mu tunda dai bana sha’awar bautan gumaka, kuma bana son ya kashe ni.” Inji Omotolani.

Sai dai shima mijin da ake kara bai musanta bukatar matar ba. Daga karshe alkalin kotun Mukaila Balogun ya amsa bukatar matar inda ya raba auren, inda ya dogara ga hujjar cewar ma’auratan basu bukatan sake zama a inuwa daya don magance matsalolinsu.

Sa’annan kuma alkalin kotun ya bada umarnin Anthony ya mika yaronsu zuwa ga Omotolani, kuma ya umarce shi daya dinga biyan ta naira dubu hudu duk wata don kulawa da yaron.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng