Waiwaye: Kyawawan hotunan Amarya Zahra Buhari
A yanzu kam za’a iya cewa Amarya Zahra Buhari yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma uwargidar matashin attajiri Ahmad Indimi, sa’annan kuma surukar hamshakin attajiri Muhammad Indimi ta zama yar gari a dakin aure.
Amma duk da haka zamuyi waiwaye, wanda hausawa kan ce ma adon tafiya, don tunawa da kasaitaccen bikin auren nata da’a aka yi a yan watanni kadan da suka gabata. Mun dauko muku wasu hotunan bikin da baku taba gani ba.
KU KARANTA: HOTUNA: Paul Pogba ya siya katafaren gidan alfarma akan naira biliyan 1 da miliyan 300
Da biki ya karato, Zahra Buhari ta tuntubi kawararriyar mai yi ma amare kwalliyar nan mai suna Huddaya don hada mata kwalliyan amarci, kuma Huddaya bata yi kasa a gwiwa ba, inda ta baiwa marada kunya ta hanyar tsantsara ma amarya Zahra Buhari kwalliya da ado na azo a gani.
Tun daga kayan sawa, zuwa kwalliyar fuska, zuwa su awarwaro da mari da duk saura kayan kyale kyale, dukkaninsu Huddaya ce ta shirya su.
Ga wani bidiyon auren Zahra na musamman:
Asali: Legit.ng