An samu matsala: Wata mata ta haifi akuya bayan shekaru uku da ciki (HOTUNA)
Wani lamari mai tsananin daukan hankali ya faru a jihar Ribas a jiya 7 Talata 7 ga watan Feburairu inda wata mata data kwashe shekaru uku tana dawainiya da tsohon ciki, amma a ranar haihuwa ta haifi dan akuya.
Wani ma’abocin kafar sadarwa ta Facebook Simeon Chukwu ne ya bada rahoton, inda yace matar ta haihu ne a asibitin Karaka dake unguwar Rumuowha Eneka na garin Fatakwal.
KU KARANTA: Hotuna 7 na yadda attajiran larabawa ke almubazzaranci da kudi
Sai dai murna ta koma ciki ga dangin matar yayin da suka samu labarin abin data haifa, wato dan akuya bayan ta fito daga dakin karbar haihuwa, a maimakon jariri, dan mutum.
Ga wasu daga cikin hotunan matar da abinda ta haifa:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng