Matsalolin Arewa: Ina mafita?

Matsalolin Arewa: Ina mafita?

– Duk da yawan Jama’an Arewacin Najeriya Yankin na fama da mugun talauci

– Ana fama da matsalar almajiranta a Arewacin Najeriya

– Ina mafitar matsalolin Arewa?

Matsalolin Arewa: Ina mafita?
Matsalolin Arewa: Ina mafita?

“Matukar a arewa da karuwai,

yan daudu dasu da magajiya.

Da samari masu ruwan kudi,

Ga mashaya can a gidan giya.

Matukar yayan mu suna bara,

Titi da Loko-lokon Nijeriya.

Hanyar birni da na kauyuka,

Allah baku mu samu abin miya.

Sun yafu da fatar bunsuru,

Babu mai tanyonsu da dukiya.

Babu shakka yan kudu zasu hau,

Dokin mulkin Nijeriya.

In ko yan kudu sunka hau,

Babu sauran dadi, dada kowa zai

sha wuya.

A Arewa zumunta ta mutu,

Sai karya sai sharholiya.

Camfe-camfe da tsibbace

tsibbacen,

Malaman karya yan damfara.

Sai karya sai kwambon tsiya,

Sai hula mai annakiya.

Ga gorin asali da na dukiya,

Sai kace dan annabi fariya.

Jahilci ya ci lakar mu duk,

Ya sa mana sarka har wuya.

Ya sa mana ankwa hannuwa,

Ya daure kafarmu da tsarkiya.

Bakunan mu ya sa takunkumi,

Ba zalaka sai sharholiya.

Wagga al’umma mai zata yo,

A cikin zarafofin duniya.

...

KU KARANTA: 'Yan Arewa sun nemi a binciki Jonathan

Kadan kenan daga cikin matsalolin Arewa daga wakar Marigayi Sa’adu Zungur a kan Arewa. Arewa dai na fama da matsaloli da dama irin su Jahilici, Talauci da dai sauran su. Ko da Arewa ta ciri tuta wajen yawa haka kuma ta ciri wata tutar wajen yawan mace-macen aure da jahilcin tsiya da yayi mana katutu ta ko ina, ban da kuma talauci.

Domin kawo karshen wannan matsala a Yankin Arewa dai dole a komawa Ubangiji da farko. Jama’a sun kara lalacewa fiye da tunani sam babu tarbiya. Duk al’ummar da mai kudi ya zama shi ke fada-a ji, to ta shiga cikin babbar matsala. Ya zama dole a komawa Ubangiji wajen komai daga kasuwanci a shago zuwa rayuwar aure a gidajen mu.

Ya zama dole kamar yadda Mawaki yace, Arewa mu so juna. Dole Arewa ta so ‘Yan uwan ta, ta kuma zauna lafiya ba tare da rikici ba, idan har ba mu yi ba, za a cigaba da yi mana dariya. Kowa dai ya san yadda su Sardauna su ka zauna da abokan zaman na su.

Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,

Zaya sha kunya nan duniya “.

“Mu dai hakkin mu gaya muku,

Ko ku karba ko kuyi dariya.

Dariyar ku ta zam kuka gaba,

da nadamar mai kin gaskiya.

Gaskiya ba ta neman ado,

ko na zakin muryar zabiya.

Karya ce mai launi bakwai,

ga fari da baki ga rawaya.

Ga kore ga kuma algashi,

toka-toka da ja sun garwaya”.

[Marigayi Sa’adu Zungur a cikin waken sa mai suna “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya”.]

Ya kuma zama dole ‘Yan Arewa su cire girman kai da kasala su nemi na kan su. Kai in dai Dan Arewa na bambadanci da roko da tumasanci ba za mu taba cigaba ba. Wannan kyashi shi ya ke kawo bakin ciki da hassada da duk wani sharri a cikin mu.

Bugu da kari kuma dole Mutanen Arewa su yi ilmi; ilmin boko da na Arabi. Idan kuma an yi Ilmi sai ayi aiki da shi, ga Masallatai amma ba imani. Dole Mutan Arewa mu san Ubangiji da kuma hanyar lomar mu, za a ga amfani Duniya da lahira. Shata yace: 'Arewa gidan dadi, amma fa sai an bar barci!'

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng