Dalilai 4 da zai sa ku fara motsa jiki, na 3 yana da matukar anfani

Dalilai 4 da zai sa ku fara motsa jiki, na 3 yana da matukar anfani

- Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce mafi yawan yawan mutane a duniya na fama da matsalar rashin motsa jiki.

- Hukumar tace bayanai ya nuna cewa kashi 80 daga cikin 100 matasa ne.

Dalilai 4 da zai sa ku fara motsa jiki, na 3 yana da matukar anfani
Dalilai 4 da zai sa ku fara motsa jiki, na 3 yana da matukar anfani

Bincike ya nuna cewa rashin motsa jiki na jawo cututtuka kamar hawan jini, cutar daji, cutar ciwon siga da sauran su.

Bayan haka wata ma’aikata da ke gudanar da ayuukanta a karkashin hukumar WHO wato ‘Global Action Plan for the Prevention and Control of NCD’ ta shawarci jama’a da su fara motsa jiki a hankali a hankali kullum har su saba .

Kungiyar tace duk mai son ya fara hakan zai iya yi ta yawaita yin aikace-aikace a gida, yawaita tafiya, tika rawa duk kafin jikin ya saba.

Tunatarwa

1. Motsa jikin na kare mai yinta daga kamuwa daga wasu cututtuka kamar shanyewar gefen jiki, cutar dajin da ke kama nonon mata da kuma dajin da ke kama gaban mutum da yawan damuwa.

2. Yana rage kiba a jiki.

3. Motsa jiki na kara karfin kashi a jikin mutum.

4. Motsa jiki yana taimaka wa mata musu dauke da juna biyu musamman wurin haihuwa.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta shawarci mutane akan tsawon lokacin da ya kamata su dauka suna motsa jiki kamar haka;

Hukumar ta ce masu shekar 5 zuwa 17 za su iya motsa jikin su na tsawon mintuna 60 ko wace rana domin zai taimaka musu ta hayar bugawan zuciyar su yadd ya kamata da kuma kara karfin kashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng