Kara da kiyashi: yadda wata tsaleliyar budurwa ke kashe samarinta

Kara da kiyashi: yadda wata tsaleliyar budurwa ke kashe samarinta

An maka wata budurwa kyakkyawa mai suna Shabu Benos yar shekaru 38 gaban kuliya manta sabo inda ake tuhumanta da kashe saurayinta mai shekaru 48, Reeves Malamba.

Budurwa Shabu
Kara da kiyashi: yadda wata tsaleliyar budurwa ke kashe samarinta

Ita dai wannan budurwa Shabu yar kasar Zambia ana zarginta ne da kashe saurayinta Malamba a ranar 30 ga wata Janairu, ta hanyar caka masa wuka a baya, inda nan da nan aka garzaya da Malamba zuwa asibiti, sai dai bai kai labari ba.

KU KARANTA: Kotu ta yanke ma yaron tsohon minista Bala Mohammed zaman gidan yari

Yansanda masu binciken lamarin sun tabbatar da cewar masoyan biyu sun yi cacar baki da juna ne, inda a yayin cacar bakin ne Shabu ta dauko wuka ta caka ma Malamba.

Kara da kiyashi: yadda wata tsaleliyar budurwa ke kashe samarinta
Shabu tare da Malamba

Dansanda mai kara ya fada ma kotu cewar a baya ma an taba kama wanda ake zargi, wato Shabu da irin wannan laifin, a lokacin data caka ma tsohon saurayinta wuka a wuya a wani katafaren shago a birnin Lusaka.

Sai dai wasu rahotannin kuma sun bayyana cewar Shabu tana kasar Afirka ta kudu yayin da aka yi kisan kan, don haka ba itace tayi kisan ba. A yanzu haka dai Shabu na rike a hannun jami’an yansanda.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel