Dalibar jami’a ta mutu yayin ziyartar wani Alhaji

Dalibar jami’a ta mutu yayin ziyartar wani Alhaji

Mutuwan wata daliba yar jami’a mai suna Joy Odama, ya bar iyayenta cikin radadi da bakin ciki da rudani.

Dalibar jami’a ta mutu yayin ziyartar wani Alhaji
Dalibar jami’a ta mutu yayin ziyartar wani Alhaji

Marigayiya Joy Odama,wacce dalibar aikin jaridar a jami’ar jihar Kross riba CRUTECH ta tafi wajen wani Alhaji Usman I. Adamu, wanda sanannen babban mai kudi ne kuma yayi mata alkawarin sama mata karatun kyauta.

Ta tafi tare da kawarta ne ami suna Elizabeth. Game da cewar mahaifiyarta, tayi Magana da ita yayinda take kokarin zuwa wajen alhajin a ranan 20 ga watan Disama 2016,bayan ya bukaceta da tayi masa wani aiki a gida.

KU KARANTA: Wani bahaushe ya hallaka yare a Legas

Mahaifiyar mai suna Mrs Philomena Odama tace:

“Yayinda karon ‘ya ta yayi na ganin Alhaji Adamu, ta fada masa cewa ta zo neman taimakonsa domin cigaba da karatunta,amma shi mutumin ya fada mata ta zo tare da mahaifiyarta zuwa gidansa.

Ni da ‘yata muka yarda da ranan da zamu je wajensa,tunda inda Alhajin ke zaune kusa da gidanmu ne. kana muka mun samu mutane da dama masu neman taimako a wajen Alhajin.

Alhajin yayi alkawarin cewa zai taimakawa yarinyata a makaranta kuma zai sama mata aikin hukumar tsaron farin hula wato Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC).

Bayan kwanaki biyu, da yamman ranan 20 ga Disamba, Alhaji yayi wata ga yarinya ta cewa ta zo ta taimaka masa da wasu ayyukan da saboda mai aikinsa bata da lafiya ta je ganin likita.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel