Malam bahaushe ya hallaka wani direba a kan N30 a Legas

Malam bahaushe ya hallaka wani direba a kan N30 a Legas

Rahotanni na nuna cewa wanda wani Malam Bahaushe dan kasuwa ya hallaka wani Bayarebe a kan N30 a Legas

Malam bahaushe

An fara wata hargitsi a ranar Litinin,30 ga watan Janairu, a titin Mojeed da ke unguwar Igando a birnin jihar Legas, wannan al’amarin ya faru ne a lokacin da wani dan kasuwa mai shekaru 40 haihuwa, Ibrahim Adamu ya hallaka wani direban bus, Lekan Adeleke.

Mazaunar ungwar da iyalin marigayin sun rufe hanyoyin da kone-kone a kan titi, kuma sun hafka wa Hausawa yan kasuwa a yankin.

A cewar wata rahoton na Punch, wannan rikicin ya auku ne a lokacin da marigayin ya saya indomie mai darajan kudi N230 daga dan wanda ake zargin da kisan a ranar Lahadi, 29 ga watan Janairu misali karfe 10.30pm na dare.

An rahoto cewa marigayin ya bada kudi N200 inda ya kuma yi alkawarin biyan sauran N30 a washe gari, amma abin bai iwa she yaron da kasuwan dadi ba.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojojin kasar Najeriya ta mamaye ko’ina a Gambia

Dan ya zanar da uban na sa, Adamu abin da ke faruwa a inda shi uban ya hafka wa matashin mai shekaru 30 da haihuwa, sanadiyar da ya sa shi direban ya buga kansa a kan kankare gefen wata gutter.

Abokin marigayin Kehinde Akinduro, ya ce Adamu yana da shago inda ya ke sayar da kayayaki, yayin da dan na sayar da indomie kusa da shagon.

Abokin ya bayyana cewa, Adeleke ya riga ya biya sauran N30 da ake zargin sa.

Yan zanga-zanga tuni suka kone shagon bayan samu labarin mutuwar Adeleke a karfe 12am a ranar Litinin.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel