Babban mashawarcin Sanata Bukola Saraki ya ajiye aiki, ko lafiya? (Karanta)

Babban mashawarcin Sanata Bukola Saraki ya ajiye aiki, ko lafiya? (Karanta)

Babban mashawarci kuma shugaban ma’aikatan dake aiki da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, wato Sanata Isa Galaudu yayi murabus, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tabbatar.

Babban mashawarcin Sanata Bukola Saraki ya ajiye aiki, ko lafiya? (Karanta)

Galaudu yayi murabus ne daidai lokacinda Sanata Bukola Saraki ya aika da takardar sanarwa ga dukkanin hadimansa da yawansa ya kai 112, inda yake sanar dasu nan bada dadewa ba zai sallame su daga aiki.

KU KARANTA: Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203

Majiya da dama sun tabbatar ma jaridar Daily Trust labarin yin murabus na Sanata Galaudu, wanda Saraki ya nada shi a ranar 23 ga watan Yuni na 2015.

Wani daga cikin majiyar ya shaida mana cewar Galaudu ya ajiye aiki ne kwatsam ba tare da bayyana wani kwakkwaran dalili ba.

Duk kokarin da mukayi na jin ta bakin Galaudu yaci tura, sakamakon baya daukan waya kuma bai amsa sakon kota kwana da muka aika masa ba. Sai dai wata majiya na kusa da Galaudu ta shaida mana tun watannin hudu da suka gabata ne Galaudu ya sanar da Sanata Saraki burinsa na ajiye aiki, kuma Sarakin ya amince.

Majiyar ta bayyana cewar don radin kashin kansa ne Galaudu yayi murabus, ba wai wani rikici bane ya sabbaba hakan, inda yace Galaudu na shirin fuskantar wasu ayyuka ne na daban wadanda basu jibanci siyasa ba.

Sai dai da muka tuntubi Kaakakin Sanata Bukola Saraki, Yusuph Olaniyonu yace bashi da masaniyar ajiye aikin Sanata Isa Galaudu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng