Hoton Buhari tare da Gwamna Amosun suna cin abinci

Hoton Buhari tare da Gwamna Amosun suna cin abinci

Jita-jita dake kara yaduwa na cewa babu mamaki lafiyar shugaban kasa Buhari ya gaza, yasa an kuma daukar hoton shi tare da dan kuran sa kuma gwamnan jihar Ogun suna cin abinci a ranar Lahadi, 30 ga watan Janairu.

Hoton Buhari tare da Gwamna Amosun suna cin abinci
Hoton Buhari tare da Gwamna Amosun suna cin abinci

Shugaban kasa na hutu a birnin Landan, amma a wani jawabi daga kakakin sa yace zaiyi amfani da daman yaga likita domin kula da lafiyarsa.

Don haka ne mutane suka canja manufar da cewa shugaban kasa na fuskantar matsalolin lafiya sosai tare da wasu dake ikirarin cewa ba mamaki ma ya mutu.

Ana ta kokarin karyata jita-jitan ta hanyar fito da hotunan shugaban kasar daban-daban tare da mutane harma da wani hoto tare da matarsa, Aisha.

Wasu yan Najeriya da dama sun bayyana cewa ya kamata a ce anyi bidiyo wanda zai nuna shugaban kasa yana magana don kawo karshen labarai marasa dadi game da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel