An kusa kashe wani Direba don yace Buhari ya mutu

An kusa kashe wani Direba don yace Buhari ya mutu

– Wani Mutumin Jihar Kano ya kashe wani Direba da mari don yace Buhari ya rasu

– Har yanzu dai wannan Direba bai san inda yake ba

– Ana ta yada rade-radin cewa Shugaba Buhari ya rasu a Asibiti

Kamar yadda Jaridar Vanguard ta fada, wani mutumi mai suna Usman Bukar ya yankawa wani Direban mota mari har sai da ya kusa mutuwa don kawai yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mutu.

Wannan abu dai ya faru ne a Jihar Delta tsakanin Direban motar haya da wani matashi mutumin Kano. Wanda abin ya faru a gaban say ace mutumin ya yankawa Direban mari ne bayan ya ji yana yada labarin cewa Shugaba Buhari ya rasu a wurin ‘yan jarida.

KU KARANTA: Rashin lafiyar Buhari: Kwadago tayi magana

Wannan mutumi dai yace za a jefa gawar Shugaba Buhari a Kogin Neja domin halittun ruwa su ci, ya kara da cewa Shugaba Buhari mugun mutum ne, nan ne fa Malam Usman ya harzuka, ya ketawa wannan mutumi wani mugun mari, yanzu haka yana can wani asibiti mai suna Temple Clinic da ke Garin Asaba.

‘Yan uwan wannan mutumi dai sun nemi rama abin da ya faru, sai dai Jami’an ‘Yan Sanda sun shiga tsakani. Andrew Aniamaka, mai magana da bakin Hukumar ‘Yan Sanda ya tabbatar da faruwar wannan abu. Yanzu haka Usman na hannu Jami’an tsaro shi kuma wannan Direba na can Asibiti bai san halin da yake ciki ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng