Ashe whatsapp na hana yara karatu

Ashe whatsapp na hana yara karatu

– Kafafen Whatsapp da BBM suna hana yara karatu

– A dalilin irin su Whatsapp ne yara ke fadi jarrabawa

– Ana samun matsala kwarai musamman a bangaren Turanci

Ashe whatsapp na hana yara karatu
Ashe whatsapp na hana yara karatu
Asali: Facebook

Daya daga cikin manyan abubuwan da ke hana yara karatu da kuma cin jarrabawa sune wadannan kafafen sadarwar na zamani irin su manhajar Whatsapp da BBM watau Black Berry Messenger.

Shugaban gidajen aika sakonni watau fas-ofis na Kasa, Adebisi Adegbuyi ya bayyana haka a Garin Jos. Mista Adegbuyi ya raba kyauttuka ne ga wadanda suka lashe gasar rubuta wasika na ‘Yan makaranta wannan shekarar.

KU KARANTA: Shugaban Kasa ya kusa dawowa

Mista Adebisi Adegbuyi yace saboda yawan amfani da irin su Whatsapp, ya sa dalibai suna fadi jarrabawar Turanci. A manhajar whatsapp ana yawan amfani ne da wani salon turanci na dabam, hakan ya gurbata asalin ilmin su na Turancin. Ga kuma uban lokaci da yara ke batawa suna kan whatsapp din.

Kwanan nan ministan ma’adanai da albarkatin Kasa na Najeriya Dr. Kayode Fayemi yayi kira ga matasan Najeriya, inda ya nemi su da su tashi tsaye haikan wajen neman na su da kuma kawo cigaban al’umma. Fayemi yace har aikin mota yayi domin yayi karatu a Kasar waje.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng