Aikin Hajjin 2017: Saudiya ta baiwa Najeriya kujerun Makkah 95, 000
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) tace masarautar kasar Saudi Arabia ta sake mayar ma Najeriya yawan kujerun aikin Hajji da aka saba bata, kujeru dubu casa’in da biya (95,000).
A yan kwanakin nan ne gwamnatin kasar Saudiya ta sanar janye dokar rage mahajjata daga kowane kasa da kashi 20 sakamakon aikin fadada masallacin harami da tayi a shekarar data gabata, inda a bara ta baiwa Najeriya kujeru dubu saba’in da shidda (76,000)
KU KARANTA: Sarkin Kano yace baiwa mace Ilimi yafi gina masallatai
Kaakakin hukumar NAHCON Alhaji Mousa Ubandawaki ne ya shaida ma jaridar Daily Trust a ranar Alhamis 19 ga watan Janairu inda yace minista kula da ikin Hajji na kasar Saudiyya Dakta Muhammed Saleh Benten ne ya sanar dasu haka bayan wata zaman tattaunawa da suka yi karamar ministan kula da harkokin kasashen waje Khadija Bukar Ibrahim a birnin Jidda, na kasra Saudiya.
Sanarwar tace “gwamnatin Saudiya ta samar da sabbin dokoki, wandan suka hada da sauyin tsare tsaren gudanar da aikin Hajj, samar da motocin sufuri ga mahajjata, samar da kananan motoci ga mahajjata a tsakanin Mina zuwa Makkah a ranakun 10 da 13 na watan Zul Hijja, tare da inganta dakunan kwanan mahajjata.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng