LABARI DA DUMI-DUMI: Jirgin yakin Najeria ya jefa bam sansanin yan gudun hijira 'bisa kuskure'

LABARI DA DUMI-DUMI: Jirgin yakin Najeria ya jefa bam sansanin yan gudun hijira 'bisa kuskure'

Wani Jirgin yakin sojin Najeriya ya jefa bam bisa kuskure a sansanin yan gudun hijira dake kauyen Raan a jihar Borno, wanda yayi sanadiyan mutuwan mutane biyu daruruwan mutane suka ji rauni.

A cewar jaridar Premium Times, an kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti don samun kulawa.

Sansanin na Rann na karamar hukumar Kala-balge ne kuma shake yake da dubunnan yan gudun hijiran Boko Haram.

Birgediya Janar Rabe Abubakar wanda ya kasance kakakin sojin ya tabbatar da mummunan al’amarin kuma cewa hukumar soji tayi danasanin kuskuren.

KU KARANTA KUMA: An tayar da bam din UNIMAID ne saboda aikin kafirci – Shekau

Ya ce lamarin ya faru ne bayan sun samu labarin cewa mayakan Boko Haram sun taru a wani waje da shirin kai hari.

"Amma a bisa tsautsayi sai ya fada wannan kauye. Ba da niyya mu kai hakan ba, kuma hakan dama kan faru a yankunan da ake yaki.''

Jami'in ya jajanta kan lamarin inda kuma ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, "amma muna ci gaba da bincike.''

Shugaban rundudar yaki da Boko Haram Manjo Janar Lucky Irabor ya shaida wa manema labarai cewa an samu mutuwa da raunuka a harin.

Ya kara da cewa har da sojoji guda biyu a cikin wadanda suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: