Masu garkuwa da mutane sun sace wani Malamin asibiti a Sokoto

Masu garkuwa da mutane sun sace wani Malamin asibiti a Sokoto

– Wani Malamin Asibiti ya fada hannun miyagu masu garkuwa da mutane a Sokoto

– Kungiyar Malaman Asibiti na Jihar Sokoto ta bayyana haka

– Satar Jama’a dai ya zama ruwan dare a Kasar nan

Masu garkuwa da mutane sun sace wani Malamin asibiti a Sokoto
Masu garkuwa da mutane sun sace wani Malamin asibiti a Sokoto

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an sace wani Malamin Asibiti a Garin Sokoto. Shugaban Kungiyar Malaman asibiti na Jihar, Abdullahi Aliyu ya bada wannan sanarwa ba da dadewa ba. Sunan wannan Jami’in Asibiti dai Bello Arzika.

Abdullahi Aliyu yace an sace daya daga cikin ‘ya ‘yan Kungiyar na sun a Malaman asibitin Najeriya watau MHUN. An sace Malamin lafiyar ne a Yau Litini kamar yadda Aliyu ya bayyanawa manema labarai. An dai yi gaba da Malamin ne bayan ‘Yan fashi sun tare su.

KU KARANTA: Za a kashe wasu 'Yan Shi'a

An sace Bello Arzika ne a hanyar Sokoto zuwa Isa kamar yadda NAN mai dillacin labarai ta bayyana. Yanzu dai an shiga Dajin Gundumi da Malamin kiwon lafiyar. Jami’an tsaro dai sun ce ba su da masaniya game da lamarin.

Sata da garkuwa da Jama’a dai ya zama ruwan dare a Kasar, haka kwanaki a ka kama wani Tsohon Malamin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a hanyar sa ta Abuja.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel