Shugaba Buhari ya jajintawa jami’ar Maiduguri

Shugaba Buhari ya jajintawa jami’ar Maiduguri

- A yau Najeriya ta waye gari cikin wani labara mai susan ciki na tashin Bam a jami’ar Maiduguri

- Ana sa ran mayakan Boko Haram ne suka kai wannan mumunan hari

Shugaba Buhari ya jajintawa jami’ar Maiduguri
Shugaba Buhari ya jajintawa jami’ar Maiduguri

Bam din ya tashi ne a cikin masallaci inda mutane 5 suka rasa rayukansu kuma wasu 20 sun jinkita. Shugaban sashen likitancin dabbobi na jami’ar, Farfesa Aliyu Mani, ya hallaka a hadarin.

Kana wata Bam din ta ske tashi a hanyar mashigar jami’ar inda mutane ke wucewa. Wannan abu ya tayar da hankalin mutane.

KU KARANTA: Kalli hotunan harin Bam da aka kai Jami'ar Maiduguri

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon jajenshi ne ta hanyar mai Magana da yawunsa Femi Adesina.

Yace: Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai jami’ar Maidguri da safiyan ann. Shugaban kasan ya jajintawa jami’ar, gwamnatin jihar Borno, da iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma mutanen jihar Borno.

Kana kuma yana gaishe da wadanda suka raunana ,yana tayasu addu’an sauki da kuma kwanciyan hankali ga iyalansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel