Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale

A ranar Lahadi 8 ga watan Janairu, labari ya karade ko ina cewa anga wasu bishiyoyi biyu dauke da sunan Allah a Abule Iroko, wani gari a Ado-Odo, Ota, dake jihar Ogun.

An rahoto cewa Micheal Ibironke, daya daga cikin mazauna gidan, yace yana zaune a gidan sama da shekaru goma sha bakwai (17) kuma ya tabbatar da cewan an shuka bishiyoyin ne a shekarar 2014, amma cewan basu taba ganin abu makamancin wannan rubutun na sunan Allah a jiki ba.

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale
Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale

Gidan wanda ke lamba 6, unguwar Unity, Ire Akari ya dade da zama karamin Makkah ga mutane dake zuwa don tabbatar da gaskiya game da rahoton.

Lokacin da hukumar Legit.ng ta kai ziyara garin da misalign karfe 10.30 na safiyar ranar Talata, 10 ga watan Janairu, don gano gaskiyar Al’amarin, mun tarar da danzazon jama’a, don haka mutanen da suka kewaye bishiyar sun isa tabbatar da cewa abun mamaki ya afku ga bishiyar zogalen.

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale
Iyaye mata kewaye da bishiyan don samun tabbaraki daga Allah

Mutane daga waje da cikin garin sun cika dauke da ledan ruwa makale a jikin bishiyar yayinda suka ci gaba da ihun kiran sunan ‘Allahu’ wato Allah mai girma.

Jim kadan bayan nan, wasu kungiyar mata suka taru karkashin bishiyan don yin addu’a, wannan ya faru ne bayan sun gama goga ruwan ledan a inda sunan Allah ya bayyana jikin bishiyan, kuma hankalinsu ya gushe a yayin hakan.

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale
Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale

Wakilinmu ya tunkari mutanen dake tsaye a kusa da bishiyan don sanin menene abu na musamman game da shi, amma basu kula mu ba ma inda suka mayar da hankulansu ga addu’an da suke yi.

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale
Kiristoci ma sun je gurin don addu'a da samun tabbaraki

Opemipo Ibironke, dan Mista Micheal (mammalakin gidan), ya yi bayanin abunda ya sani kan bishiyar.

Ya fada ma Legit.ng cewa ya shiga al’ajabi a lokacin da ya ga rubutun larabcin a jikin bishiyarsu, cewa abune da zai karyata da ace ba akan idannunsa abun ya afku ba.

Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale
Sunan Allah ya bayyana a jikin bishiyar zogale

“Mahaifiyata taji labarin rubutun dake kan bishiyar zogalen a waje yan kwanaki da suka wuce don haka tazo don ta dunba ko akwai abu makamancin haka a harabar gidan (saboda bishiyar zogale biyu ne damu).

“Ta duba karamin amma bata ga komai ba, amma da ta duba babban, ta kira kowa don a fito a gani,” yayi bayani.

Da aka tambaye shi wanda yake zaton ya sanya rubutun a jikin bishiyar, matashin ya nace kan cewa baida masaniyan abunda ya faru, amma baya tunanin wani ne ya yi rubutun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng