Gawa ta ki rami: Akwatin gawa ta karye, gawa ya faɗo
Yayin da ake cikin jimamin mutuwar wani mutumi dan kasar Afirka ta kudu mai suna Sibusiso Dlamini, jama’a yan zaman makoki an taru, kwatsam sai wani abin ban mamaki ya faru.
Abin daya faru kuwa shine, daidai lokacin da gwanayen daukan makara suka daga makarar Dlamini sama cancaka kan hanyarsu ta zuwa makabarta, sai makarar ta rufta, gawar kuma ta fado kasa da karfi, Tim!!
KU KARANTA:Soyayya: Sabbin ma’aurata a sansanin yan gudun hijira sun samu tagomashi
Koda jama’a suka ji karar faduwar gawar, sai kowa ya ranta a na kare, kira suke kafa mai naci ban baki ba? A tunanin su gawar ce ta tashi. Sai dai abinka da yan’uwa, nan da nan danginsa suka suture ta shi, suka rufe shi da bargo kafin ma’aikatan daukan gawar su sake dauko wani sabon akwatin gawa.
Sai dai iyalan Dlamini sun nuna bacin ransu matuka da abin da ya sami dan uwansu, an jiyo wani daga cikinsu yana fadin, “wannan cin zarafin Sibusiso ne, kuma cin mutunci ne ga magabatan mu. Sibusiso mutumin kirki ne, bai kamata hakan ya same shi ba.”
Daga bisani an binne Sibusiso washe gari bayan hakula sun kwanta.
ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng