Soyayya: Sabbin ma’aurata a sansanin yan gudun hijira sun samu tagomashi
A ranar Lahadi 8 ga watan Janairu ne jami’an hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) suka daura ma wasu masoya aure a sansanin yan gudun hijira dake Yola, jihar Adamawa.
Masoyan da aka fara daura ma aure sune Abdu Kanuma da amaryarsa Fanta Mohammed, yayin da na biyun kuwa sune Ango Baba Goni da Falta Babagoni a matsyain amaryarsa.
KU KARANTA:Kwanaki 1000 da sace yan matan Chibok: Buhari yayi alkawarin dawo dasu
Hukumar NEMA ta mika musu kyautana kayayyakin abinci da sauran kayayyakin amfani don su tabbatar da tsaftan jikkunansu.
Cikin kyautukan da suka samu sun hada da kwalayen taliyar Indomie, man shampoo, madara, ruwan roba, sabulun wanka da sauransu.
Allah ya basu zaman lafiya
Ku cigaba neman labaran mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng