Mutane 2 sun rasa rayukansu, biyu sun bata a sabon harin da aka kai Kudancin Kaduna

Mutane 2 sun rasa rayukansu, biyu sun bata a sabon harin da aka kai Kudancin Kaduna

- Sanata Danjuma Tella Laah, dake wakiltan Kaduna ta Kudu, ya maganta kan sabon hari da kashe-kashe da Fulani makiyaya suka yi

- Rahotanni ya nuna cewa an kashe akalla mutane biyu kuma an kaddamar da batan wasu mutane biyu a sabon harin da aka kai Kudancin Kaduna

- Sabon harin yayi barazana ga burin dawo da zaman lafiya ga yankin Kudancin jihar Kaduna dake cike da tsoro

Mutane 2 sun rasa rayukansu, biyu sun bata a sabon harin da aka kai Kudancin Kaduna
Mutane 2 sun rasa rayukansu, biyu sun bata a sabon harin da aka kai Kudancin Kaduna

Wasu yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kashe akalla mutane biyu a sabon harin da suka kai Kudancin Kaduna, jaridar The Guardian ta ruwaito.

An gudanar da kai harin ne a ranar Asabar, 7 ga watan Janairu a kauyen Tsonje, kusa da garin Kagoro a karamar hukumar Kauru.

Sanata Danjuma Tella Laah, dake wakiltan yankin Kaduna ta Kudu, a wata sanarwa da yayi a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, a Kaduna, ya tabbatar da al’amarin kuma yayi korafi a kan sabon hari da kashe-kashe da Fulani Makiyaya suka kai.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta damke azzakarin abokin cinikinta kan bashin N100

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa sabon harin yayi barazana ga burin dawowar zaman lafiya ga yankin na Kudancin Kaduna dake cike da tashin hankali.

A halin da ake ciki, an kashe manoma biyar a wani hari na daban da ake zargin Fulani Makiyaya ne suka kai a garuruwa guda biyu a jihar Delta.

Southern City News ta ruwaito cewa an gudanar da harin ne a Abraka da Obiaruku a gabas Ethiope da karamar hukumar Ukwuani na jihar, an kuma yi na’am da cewan Fulani makiyaya ne suka kai harin.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: