Barka: Yar shekara 64 ta samu haihuwa na biyu a kasar Sin
A ranar Laraba 28 ga watan Disamba ne wata tsohuwa mai shekaru 64 ta haihu, haihuwa na biyu a kasar Sin.
Sai dai tsohuwar da ake tunanin itace uwa mafi tsufa a Duniya ta haihu ne bayan anyi mata tiyata. Kuma cikin ikon Allah likitoci sun samu nasarar fitar da jaririn ba tare da wata matsala ba.
Yayin da take jawabi, likitan da tayi ma tsohuwar tiyata Teng Hong tace, matar itace mace yawan shekaru data taba yi ma tiyatan haihuwa, wata kila ma ta kasance mafi shekaru data taba haihuwa a kasar Sin.
KU KARANTA:Miji ya wurgo matarsa daga saman bene saboda ta cika yawo
Likitan tace: “na ji tausayin matar matuka, kuma hankalina ya kwanta ganin yadda matar da jaririn nata suke cikin koshin lafiya sosai. Zamu sallame sun an da yan kwanaki kadan.
Barka.
Zaku iya tuntubar mu a nan ko a nan.
Asali: Legit.ng