Wani mutum mai shekara 30 ya aure mata biyu a rana daya (hotuna)

Wani mutum mai shekara 30 ya aure mata biyu a rana daya (hotuna)

- Anyi wa wani matashi daurin aure mata biyu a rana daya

- Mallam Dahiru mai shekara 30 ya hada daurin aure mata biyu a lokaci daya

Ango da amarya

Mallam Isyaka Dahiru wanda ya kammala karatun digiri na Accountancy daga Federal Polytechnic, Nasarawa, ya yi daurin aure da mata biyu a rana daya gab da sabuwar shekara.

Da wanna auren yanzu matan mallam Dahiru ta tashi zuwa uku.

Wani mutum
Wani mutum mai shekara 30 ya aure mata biyu a rana daya (hotuna)

Mallam Dahiru ya nuna wadannan hotunan daurin aure a shafin za na facebook da amarya Khadijat da kuma Rashida.

Ango, wanda aka haifa a ranar yuni 23, 1987, ya gayyaci mabiyan za a shafin facebook zuwa ga daurin auren za da Khadijat da kuma Rashida a ranar disamba 31, 2016 a gidan mallam Muhammad Adi a bayan makarantar RCM na garin Doma ta jihar Nassarawa a karfe 10 na safe.

Wani mutum
hotuna

Bikin aure na biyu ya faru sa'a daga baya a ranar.

Rahoto daga “Daily Nigerian” ta nuna cewa ba ta samu damar ganawa da masu auren ba saboda hidimar biki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng