Minista Solomon Dalung ya gargadi ‘Yan wasa

Minista Solomon Dalung ya gargadi ‘Yan wasa

– Ministan Wasanni na Kasar, Solomon Dalung yace Gwamnati ba asusun ‘Yan wasa bane

– Ministan yace ‘Yan wasa su daina tambayar Gwamnati kudi

– Dalung ya bayyana irin kalubalen da ya samu a Ma’aikatar sa

Minista Solomon Dalung ya gargadi ‘Yan wasa
Minista Solomon Dalung ya gargadi ‘Yan wasa

Ministan wasanni na Najeriya, Solomon Dalung yace ‘Yan wasan Kasar su daina tambayar Gwamnati kudi don ba su bada ajiya ba. Dalung yake cewa Gwamnati fa injin ATM bane mai aman kudi.

Ministan ya bayyana haka ne ga ‘Yan Jarida a Garin Jos. Yace dole fa a fahimci cewa ba aikin Ma’ikatar wasanni bane raba kudin ‘Yan wasa da sauran su. Yace akwai Kungiyoyi na wasannin da wannan aiki ya rataya a kan su. Solomon Dalung Yace tsakanin su da Gwamnati sai da a raba gardama.

KU KARANTA: Don Allah ku bar mu mu tsere-Biyafara

Solomon Dalung yace idan har ana bukatar kudi a Ma’aikatar dole sai an aikawa Shugaban Kasa wanda sai ya amince sannan Ma’aikatar kudi da sauran masu ruwa –da-tsaki za su saki kudin zuwa Ma’aikatar wasannin.

Kwanaki dai ‘Yan wasan Najeriya sun yi zanga-zanga bayan sun ci kofi ba a biya su kudin su ba. Ministan wasanni na Najeriya, Solomon Dalung yace sun koyi darasi a takaddamar da ta faru tsakanin su da ‘Yan wasan na Super Falcons.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel