Honarabul Jibrin yace babu maganar sulhu

Honarabul Jibrin yace babu maganar sulhu

– Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Tarayya, Abdul Jibrin ya bayyana cewa har yanzu yana kan bakan sa

– Jiya an rahoto cewa ya shirya zama domin ayi sulhu da Shugaba Yakubu Dogara

– Hon. Jibrin yace wannan karyar banza ce, asali ma yanzu ya fara

Honarabul Jibrin yace babu maganar sulhu
Honarabul Jibrin yace babu maganar sulhu

Dogara: Honarabul Jibrin yace babu maganar sulhu

A jiya da rana ne Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Hon. Abdulmumuni Jibrin wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji na Jihar Kano ya shirya yin sulhu da Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara.

A jerin wasu sakonni da Dan Majalisar ya aika ta shafin Twitter, ya bayyana cewa wasu daga cikn yaran Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara ne da wannan danyen aiki. Jibrin yace Turaki Hassan ne ya yada wannan rade-radin na karya. Yace yana nan kan bakan sa, babu gudu-ba ja da baya.

KU KARANTA: Fayose ya shiga uku ya lalace

Honarabul Jibrin yace babu wani sasantawa da yake kokarin yi da Kakakin Majalisar; Yakubu Dogara ko ta wasu ‘Yan Majalisar ko Dattawan Kasar kamar yadda ake rade-radi. Yace nan gaba kadan ma zai tona wasu asirin.

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta tsige Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abdulmumuni Jibrin bayan da ya zargi Shugaban Majalisar wakilan Kasar, Dogara Yakubu da wasun su da laifin handame wasu kudi daga kasafin bana.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel