Hukumar SSS tayi wawan kamu
– Jami’an Hukumar SSS sun yi wani babban kamu a Najeriya
– Jami’an sun kama wasu ‘Yan fashi masu tare ‘Yan Kasar waje a Kasar
– An samu nasarar karbe kayan da suka sace a Abuja
Hukumar ‘Yan Sanda na sirri na Najeriya watau SSS sun yi nasarar kama wasu ‘Yan fashi da makami wadanda suka saba tare ‘Yan Kasar waje a Kasar a Babban Birnin Tarayya watau Abuja.
Hukumar tace ta damke Ikechukwu Obadiegwu da takwaran sa Ikechukwu Eke bayan wani bincike da tayi. Yanzu haka an samu nasarar karbe duk abubuwan da suka sace a Abuja. Wadannan ‘Yan fashi dai ba su tare kowa sai Mutanen Kasar waje.
KU KARANTA: A guji shinkafar roba-NAFDAC
Jaridar Premium Times ta rahoto Jami’in da ke magana da bakin Hukumar yana cewa yanzu haka an damke wadannan hatsabiban ‘Yan fashi a Abuja. Mista Tony Opuiyo yace yanzu haka suna hannu. Hukumar kuma ta damke wani Dan Kano mai suna Auwal Yakasai, wanda ya taba gaba da fiye da Miliyan 100 na Bankuna.
Kwanan ne kuma Shugaban Kasar Amurka, Barrack Obama da kan sa ya jinjinawa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya bayan da Jami’an tsaron Kasar na DSS suka gano wani yunkurin kai harin ta’addanci a Kasar Amurka.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng