Gwamnan Plato ya koki arziki kan ‘yan bindigar da suka kashe mutane 484 a shekarar 2010

Gwamnan Plato ya koki arziki kan ‘yan bindigar da suka kashe mutane 484 a shekarar 2010

- Gwamnan jihar Plateau ya roki mutanen da ke zaune a garin DogoNahawa da su yafewa ‘yan bindigar da su ka kashe mutane 484 a 7 watan Maris, 2010

- Lalong ya kuma zaburar da mutanen yankin a kan su ci gaba da yiwa mamatan adduo’i

- Ya kuma bayar da tabbacin gyara dukkanin kayayyakin da aka lalata

Gwamnan Plato ya koki arziki kan ‘yan bindigar da suka kashe mutane 484 a shekarar 2010
Gwamnan Plato ya koki arziki kan ‘yan bindigar da suka kashe mutane 484 a shekarar 2010

Gwamnan na jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya nemi mutanen garin Dogo Nahawa da su yafewa wadanda suka kashe darurruwan ‘yan uwansu domin samun zaman lafiya.

Iftila’in wanda ya faru a 7 ga watan Maris, 2010, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 484 wanda ya hada da mata, da kuma kananan yara masu yawa, a lokacin da wadanda ba a san ko su waye ba suka kai hari cikin garin.

Kusan shekaru shida ke nan da afkuwar lamari, amma har yanzu mutanen da aka kashewa ‘yan uwa da abokai ba su samu an yi musu adalci ba.

Gwamnan jihar na Plateau yana rokon munaten da su yafewa wadanda suka kashe mutanen har 484 a 2010.

Lalong, wanda ya ziyarci garin domin yin murnar bikin kirsimeti tare da iyaye mata da maza da kuma marayu, tare da rakiyar wasu kusoshin gwamnati, wanda suka hada da sakataren gwamnati, Cif Rufus Bature, da kuma shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Jos ta kudu, Mista Augustine Pwakim, ya ba su shawara da su bar wa Allah komai.

Gwamnan yace: "abin da za mu iya cewa, shi ne kawai Allah ya jikan wadanda suka rasu, amma ina kira a gareku da ku cigaba da samun zaman lafiya mai dorewa.”

Gwamnan ya kuma yabawa Apostle Eugene Ogu, shugaban gidauniyar ‘Arm of Hope,’ da ke garin Fatakwal, domin bude makarantar gaba da firamare ta farko a yankin.

Kamar yadda jaridar Guardian wacce ta rawaito labarin ta ce, gwamna Simon Lalong ya alkawarta gyaran dukkanin abubuwan da aka lalata. Mutanen yankin sun ce an yi watsi da su, har sai da wani gidan yada labarai ya yi magana kan kashen-kashen na shekarar 2010 tukunna.

Shugaban na makarantar yankin daya tilo, wacce ita ma aka lalatata, Esther Samson, ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka musu da kayan aiki, kamar su, dakin gwaje-gwaje, da kuma Kwamfutoci, ta kuma kara da cewa, makarantar har yanzu ba ta sami shedar amincewa daga hukumar shirya jarabawa ta Afirika ta yamma ba watau WAEC, da kuma ta cikin gida (NECO).

Asali: Legit.ng

Online view pixel