Buhari, Saraki na cikin wani ganawar sirri a Aso Rock
Rahotanni sun ce a yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin wani ganawar sirri tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
A cewar jaridar Daily Trust, ana gudanar da ganawar ne a fadar shugaban kasa a Aso Rock, Abuja kuma ya fara ne da karfe 12.00 na rana lokacin da shugaban majalisar dattawan ya iso.
KU KARANTA KUMA: Karda ka barmu mu mutu a karkashin Buhari – MASSOB ga Donald Trump
An bayyana cewa Saraki bai zanta da manema labarai ba kamar yadda kai tsaye ya wuce ofishin shugaban kasa don ganawar.
Har yanzu ba’a sanar da cikakken bayani game da taron ba amma ana hasashen cewa ba zai rasa alaka da matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu ba da kuma sauran muhimman al’amuran kasar.
Asali: Legit.ng