Kotu ta yankewa dan Hakimi a jihar Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yankewa dan Hakimi a jihar Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar kutun majistare a jihar Katsina dake a garin Funtuwa a ranar Alhamis ta yankewa Mu'ammar Tukur da ga tsohon Hakim Bakori, kisa ta hanyar rataya, bisa kamasa da laifin kisan gilla.

Kotu ta yankewa dan Hakimi a jihar Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kotu ta yankewa dan Hakimi a jihar Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya

Tukur mai shekaru 32 wanda mahaifinsa ya yi danmajalisaar tarayya Abuja mai wakiltar Bakori da Danja, ya yi amfani da wuka wajen dabawa Shafir Muktar wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa har lahira.

Alkalin da ya yanke hukubcin mai shari'a Abbas Bawale ya bayyana cewa karar da Mr. Aminu Garba wake jagoranta tana dauke da gamsassun hujjoji har guda biyar kwarara tare da shedu guda biyar da kuma uwa uba gawar da aka kashe, abinda ya kawo kisan da kuma niyyar kisan kan.

Alkalin ya kara da bayyana cewa lamarin ya faru ne a watan Afirilun 2008 a yayin wata 'yar hatsaniya a tsakaninsu inda ya kuma aikata kisan a gaban shedu a wani wurin matattarar jama'a.

Sai dai alkalin ya ce lauyan dake kare wanda ya aikata laifin ya yi turjiya wajen kin amincewa da kwararan hujjoji da dalilan da aka gabatar masa.

Mai shari'ar ya kuma bayyana cewa wanda ya aikata kisan ya ranta a na kare tun ranar da lamarin ya faru 2008 har sai a ashekarar 2013 aka yi nasarar cafke sa a yayin da wata gwaggwansa ta rasu wajen zana'idar matar.

A don haka mai shari' ar ya yi watsi da bangaren mai kare shi inda ya bayyana cewa , hujjojin da mai kare shi ya kawo ba gamsassu bane domin mi ya sa wanda ake zargin ya gudu ya bar garin bayan lamarin ya faru, sannan kuma ya zo da wukar karfe domin ya aikata kisan.

Daga karshe dai bayan dogayen hujjojin da kotu ta bayar ta yankewa Mu'ammar Tukur hukuncin kiss ta hanyar rataya.

Ya kuma shawarci wanda aka yankewa hukunci da cewa zai iya daga kara kamin nan da kwana 90.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng