Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)

Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)

Kasantuwar harkar buga wasan kwallon kafa hark ace dake kawo makudan kudade, wannan ke sanya yan kwallo, musamman shahararru a cikinsu yin sharholiyarsu ta hanyar siyan motoci masu tsada da siyan gidajen alfarma masu cike da kawa da ado.

Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)

Kwatankwacin haka ne Cristiano Ronaldo yayi, inda ya siya wata gawurtacciyar motar hawa da kudinta ya kai naira miliyan 37 don nuna farin cikinsa da shekarar 2016, wanda a cikin ta ne ya samu nasarori da dama.

KU KARANTA:Tsohon dan wasan kwallon kafa na Afirka ya samu sarautar gargajiya

Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)
Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)

A wannan shekarar ne Ronaldo ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai, kofi na musamman na gwanayen nahiyar Turai, kofin kungiyoyin kwallon duniya, sa’annan ya lashe kyautan zakaran kwallon kafa a karo na 4, da wannan ne shi kansa Ronaldo yake ganin bai taba samun nasarori a kwallo ba fiye da yadda ya samu a bana.

Ronaldo ya siya motar naira miliyan 37 (Hotuna)

A yanzu dai Ronaldo ya samu hutun Kirismeti daga kungiyarsa ta Real Madrid kafin su fara atisaye a ranar Laraba, hakan ya sanya dan wasan daura hotunan sabuwar motar tasa kirar Marsandi AMG GLE da farashinta ya kai €115,000 a shafinsa na Instagram, kimanin N37m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel