An fitar da sabbin sharuddan aikin hajji (Karanta)

An fitar da sabbin sharuddan aikin hajji (Karanta)

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta fitar da wasu sabbin sharudda da ta ce dole ne, duk wani maniyyaci ya cika su kafin ba shi damar zuwa aikin hajji a Saudiya.

An fitar da sabbin sharuddan aikin hajji (Karanta)
An fitar da sabbin sharuddan aikin hajji (Karanta)

A cewar shugaban sashin hulda da kafafen yada labaran hukumar, Alhaji Uba Mana, sharudan za su taimaka wajen kawo karshen samun masu safarar miyagun kwayoyi da ke shiga cikin maniyatan Najeriya, da kuma aikata sauran laifuka a yayin aikin hajji.

Mana ya ce yanzu tilasne maniyyaci ya gabatar da wani sahihin mutum, da zai tsaya masa kafin ba shi damar zuwa aikin hajji, wadanda suka hada da, limamin masallacin Juma’a da ma’aikacin gwamnati da ke mataki na 12, ko kuma mai mukamin sarautar gargajiya.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya fallasa cewa har yanzu basu san inda akayi da wasu Naira milyan N500 da tsohohuwar Gwamnatin Jonathan ta ware domin sake gina makarantar Chibok da harin Boko Haram ya lalata.

Idan dai ba'a a manta ba, ministar kudi a zamanin gwamnatin Jonathan Misis Ngozi Okonjo-Iweala, ta ziyarci garin na Chibok a watan Maris din 2015 domin kaddamar da aza harsashin gyaran ginin makarantar wacce aka kiyasta zata lashe kimanin milyan N500.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng