Sarauniyar Ingila zata yi murabus a karshen shekara, ko me yasa?

Sarauniyar Ingila zata yi murabus a karshen shekara, ko me yasa?

Mai girma sarauniyar Ingila, wato sarauniya Elizabeth II zata yi murabusa daga jagoranci kungiyoyi daban daban da take yi da yawansu ya kai 600 a karshen shekarar nan.

Sarauniyar Ingila zata yi murabus a karshen shekara, ko me yasa?

Idan ba’a manta ba dai sarauniya Elizabeth ta dare gadon sarauta ne tun a shekarar 1952, inda ta kwashe shekaru 64 tana mulkin masarautar Birtaniya. Sarauniyar ta kere tsawon shekarun da kakarta sarauniya Victoria tayi tana mulki.

Sa’annan a yanzu itace mai sarautar da tafi dadewa a duniya tun bayan mutuwar sarkin Thailand Sarki Bhumibol Adulyadej.

Sarauniyar Ingila zata yi murabus a karshen shekara, ko me yasa?
Sarauniyar Ingila tare da shugaba Buhari

A karshen watan Disambar bana, 31 ga watan ne sarauniya zata yi murabus daga jagorantar wasu kungiyo sama da 20 cikin sama da kungiyoyi 600 da take jagoranci. A watan Afrilun daya gabata ne sarauniya Elizabeth ta cika shekaru 90 a rayuwa, ita zata bi sahun mijinta hakimin Edinburgh wanda a kwanakin baya yayi murabusa daga wasu kungiyoyi da yake jagoranta a shekarar 2011.

KU KARANTA: Labari mai daɗi: Gwamnan jihar Legas zai fara siyar da shinkafar LAKE a yau

Cikin sanarwar da aka fitar daga fadar Buckingham a ranar 20 ga watan Disamba, Sanarwar tace: “A karshen shekarar nan ne sarauniya za tayi murabus daga shugabancin kungiyoyi da dama, inda za’a mika ragamar tafiyar da ire iren kungiyoyin nan ga yayan gidan sarauta nan bada dadewa ba.”

Wasu daga cikin kungiyoyin da sarauniya zata fita daga ciki sun hada da: Battersea Dogs and Cats Home, Barnardo’s, the All England Lawn Tennis and Croquet Club and Wimbledon Lawn Tennis Association.

Sarauniya Elizabeth ta kwashe shekaru 69 tare da mijinta Duke, kuma sun haifi yaya hudu, sa’annan suna da jikoki takwas, da tattaba kunne biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng