Rikicin kabilanci a Taraba ya hallaka mutane 42

Rikicin kabilanci a Taraba ya hallaka mutane 42

Mutane 42 ne suka rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Taraba a inda ake zargin Fulani da kai harin ramuwar gayya kan 'yan kabilar Tibi a wasu kauyukan jihar da ke makwabtaka da jihar Binuwai

Rikicin kabilanci a Taraba ya hallaka mutane 42
Rikicin kabilanci a Taraba ya hallaka mutane 42

Rahotanni daga jihar Taraba na cewa, kimanin mutane 42 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke a tsakanin ‘yan kabilar Tibi da kuma Fulani a kauyen Sabon Gari da kuma Dan-Anacha.

A cewar jaridar Premium Times, wasu karin mutane da yawa sun yi batar dabo a yayin barkewar rikicin na baya-bayan nan a jihar. Wata majiya daga yankin na cewa, an soma rikikcin ne a ranar Asabar a lokacin da aka tsinci gawawwakin wasu Fulani biyu aka hallaka aka kuma yar a daji, wanda hakan ya sa shugabannin fulanin daukar fansa kan ‘yan kabilar Tibi.

Wani mazaunin yankin ya fadawa manena labarai cewa, ya kirga gawawakin mutane 20 wadanda aka kashe a safiyar ranar Lahadi. Sannan ya kuma ce, “mata da yara kanana da yawa sun bace ”

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Taraba David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce, rundunar ta kara yawan jami’anta a yankin don maido da bin doka da oda. Ya kuma ce ba zai iya fadin yawan wadanda suka mutu ba, da kuma wadanda suka jikkata a fadan.

A rahotan jaridar The Nation ta ce, kisan manoma da ake zargin Fulani da yi a karamar hukumar Gassol, ya sa mutane da yawa yin kaura zuwa kauyukan ‘yan kabilar Tibi, duk da kasancewar ‘yan sanda da sojoji a yankin. Wani taron samar da zaman lafiya da kwamishinan ‘yan sandan jihar Yunas Babas ya yi da shugaban kungiyar ‘yan kabilar Tibi, Goodman Dahida, da shugaban kungiyar Miyetti Allah, Lamidon Gassol da kuma sauran hukumomin jami’an tsaro bai yi tasiri ba.

A ziyarar gani da ido jaridar The Nation ta kai yankin a yammacin ranar Litinin 19 ga watan Disamba, ta ce, an kashe mutane 6 a kauyen Sabon Gari, an kuma hallaka wasu 16 a sauran kauyukan da ke yankin, ciki har da wasu mata biyu , a cewar wani da ya gani da idonsa. Daruruwan ‘yan kabilar Tibi ne suka yi gudun hijira daga Dan-Anacha zuwa na jihar Taraba zuwa wasu kauyuka a jihar Binuwai a inda kabilarsu tafi yawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel