‘Yan shaye-shaye sun kashe dan sanda

‘Yan shaye-shaye sun kashe dan sanda

– Wasu ‘Yan shaye-shaye sun kashe wani Jami’in Dan Sanda

– Dan Sandan ya gamu da ajalin sa ne lokacin da yake kokarin kama mutanen suna shan wiwi

– Marigayin ya kama su ne suna shan tabar wiwi

‘Yan shaye-shaye sun kashe Dan Sanda
‘Yan shaye-shaye sun kashe Dan Sanda

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Enugu ta tabbatar da cewa an kashe wani Jami’in ta na ‘Yan Sanda a Jihar. Wannan abu ya faru ne a Ranar Asabar da yamma kamar yadda Hukumar Dillacin labarai na Kasa NAN ta fada.

Wannan abu ya faru ne karshen wannan makon a wata babbar kasuwa ta Garin. Hukumar NAN tace ‘Yan shaye-shaye ne suka ga bayan dan sandan lokacin yana kan aiki. Masu shaye-shaye suna cikin maye lokacin da suka yi amfani da makami suka kashe Jami’in tsaro.

KU KARANTA: Sabon tashin hankali a Arewa

Babban Jami’in Hukumar ‘Yan Sandan, Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar wannan abin takaici. Jami’in yace Hukumar ta fara bincike game da lamarin. Haka kuma Hukumar tace ba ta ji dadin wannan abu ba. An kashe Jami’in ne lokacin da yake kokarin kama mutanen suna shaye-shaye.

Kwanaki aka gurfanar da wani matashi dan shekara 30 mai suna Tunde Ajani a gaban Kotun Majistare da ke Apapa na Garin Legas da laifin tada fitina da kuma yi wa wani Dan Sanda dukan tsiya. Hakan dai ta sa aka yankewa saurayin dauri a Gidan Yari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel