Manyan jaruman Kannywood maza 10 a shekarar 2016
A daidai lokacin da shekerar 2016 take gangarowa domin wucewa, inda muke tunkarar sabuwar shekarar 2017. Shine mukayi nazari tare da zakulo jarumai 10 da suka baje kolin basirarsu a farfajiyar shirya finafinan Hausa, watau Kannywood na wannan shekara.
1. Ali Nuhu
Sarki Ali, kamar yadda masoyansa suka yi masa lakabi, ba ya bukatar dogon bayani game da yadda yake jan zarensa a masana’antar shirya finafinan Hausa, watau Kannywood. Yana da mabiya sama da 337,000 a shafin Instagram, yak are karatunsa daga jami’ar Jos, fannin ilimin kasa (geography). Shine jarumin Kannywood na farko da aka tantance a shafin Twitter. Ya fito a fina-finai da dama a shekarar 2016.
Ya samu lambar yabo a Afronolly Awards na shekarar 2015 a kasar Amurka, an kuma gayyace shi a matsayin bako na musamman a taron wannan shekarar.
Dan wasan mai shekaru 42 ya kasance shugaban kungiyar shirya fina-finai na FKD, ya kuma kasance yana jin yaruka da dama kamar su Hausa, Turanci, Hindu, da French sosai.
Daga cikin wasannin da ya fito a shekarar nan sun hada da Muradin raina, Akasi, Matar Bahaushe, Mu’amalat, Gobarar Mata, Bani Bake da kuma Gamu Nan dai.
2. Sadiq Sani Sadiq
Wannan jarumi cikin ‘yan shekaru yana taka rawar da yake tserawa tsara a tsakanin takwarorinsa, musamman yadda yake iya juya kansa zuwa siffofi daban-daban a cikin finafinai. Sadiq mai shekaru 35 wanda ya shiga harkar fim a shekarar 2013 ya nuna bajinta a cikin fim din DANMARAYAN ZAKI, wasan da ya kunshi manyan jaruman Kannywood maza da mata.
Ya auri Murja kanwar tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema
In 2016, Sadiq won the best actor in the Kannywood awards and BON award for best actor in December. Sadiq was spectacular in the movies Wani Gari, Mati da Lado, Hanyar Kano, Takanas Ta Kano, Ruma and many others. He has over 206,000 fans on Instagram.
A shekarar 2016, Sadiq ya lashe zaben gwarzon jarumin Kannywood a watan Disamba. Sadiq ya fito a fina-finai irinsu Wani Gari, Mati da Lado, Hanyar Kano, Takanas Ta Kano, Ruma da sauransu. Yana da mabiya sama da 206,000 a Instagram.
3. Adam Zango
Yariman Zango kamar yadda akeyi mai lakkabi, yana juya akalar abubuwa uku, ya kasance furodusa, dan wasa, sannan kuma yana da fasahar waka da rawa. Fuskarsa ta haske a 2016. Shi ne mallakin White House Musical Records, kuma shugaban Prince Zango Productions. Shine tauraro a fim din HINDU. Ya fito a fina-finai kamar su Rabin Raina, Basaja, Gwaska, Uzuri, Yar’Amana da sauransu. Yana da mabiya 270,000 a Instagram.
4. Rabiu Rikadawa
Rabiu wanda aka fi sani da Dila, ya kasance uba a Kannywood, saboda mafi yawan rawar da yake takawa ya kasance na uba. Rabiu yay i tashe a wasannin irinsu Takanas Takano, Akasi, yar’adaidaita, Bashi hanji ne da kuma Zinaru. Jarumin na da mabiya 60,000 a Instagram.
5. Suleiman Bosho
Idan ana batun finafinan ban dariya a masana’antar finafinan Hausa a yanzu babu kamar sa. Duk ta inda aka bullo sai ya bulle domin ya nishadantar da ‘yan kallo.
Salon barkwancin da ya fito da shi ya rage wa masoya kallon finafinan Hausa radadin rasuwar Rabilu Musa Ibro shekaru biyu da suka gabata. Jarumin na da mabiya 3,000 a Instagram.
Ya fito a Basaja, Kujerar tsakar gida, Mahaukaciya, Masu Gudu Su Gudu.
6. Nuhu Abdullahi
Babu shakka yanayin da jarumin ya fito a cikin Fim din FURUCI ya gamsar da kaso 90 cikin 100 na mutanen da suka yi sharhi a kai. Hakika Nuhu ya nunawa duniya cewar lallai ya kawo karfi da zai iya yin gogayya da manyan jaruman Kannywood. Yadda ya bayyana a matsayin dan tasha, ba shi da tsoro, duk abin da zai da karfin zuciya yake aikata shi. Yayin da mutum yake kallo, yana iya mancewa fim ne ko kuma gaske.
Bayan nasarar da ya samu na shiga sahun jaruman da ake labarinsu sakamakon rawar da ya taka a fim din Furuci, Nuhu Abdullahi ya fara haskakawa a finafinan Turanci, wanda labaransa ke da alaka da zamantakewar rayuwar Hausawa.
Finafinan Turanci guda uku da ya fito a ciki, THERE IS A WAY, LIGHT AND DARKNESS da kuma THORNY, sun kara tabbatar da cewar shekarar 2016 ta zo wa jaruman da babbar nasara, ta yadda ba zai iya mantawa da ita ba.
7. Yakubu Mohammed
Fim din Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE, na cikin jerin finafinan Yakubu ba zai manta da su ba a rayuwarsa ta duniyar nishadi. Duk da cewar shirin an yi shi ne da harshen Turanci, amma hakan bai hana Fim din mamaya a Arewacin Nijeriya ba.
Yakubu Muhammad ya fito a dan gidan attajiri, wanda ba ya shakkar murza Naira a kasa. Rawar da ya taka ce ta sanya shi zamowa cikin wannan jeri a matsa yin na bakwai.
8. Falalu Dorayi
Tare da zama da mabiya 121,000 a Instagram, Falalu Dorayi na daya daga cikin gwarazan jariuman Kannywood kuma babban darakta. A wannan shekarar Dorayi ya wuce yanda ake zato, yay i barkwanci a fim din Dankuka, Ramlat, Hudu Bazara, Na Hawwa, Umar sanda da sauransu.
9. Ado Gwanja
Ado Gwanja ya kasance daya daga cikin jaruman Kannywood wanda ke haskawa a kullun a cikin wasan san a Dankuka. Wannan kyakyawan jarumin ya nuna bajinta. Bisa ga wani hasashe na fim, Dakuka ya kasance wasa mafi karbuwa a Kannywood a 2016. Ya kasance sabo a harkar Instagram yana da mabiya sama da 2000.
10. Ahmad Ali Nuhu
Gado ba karanbani ba, Ahmad ya kasance da ga shahararen jarumin Kannywood, Ali Nuhu.
Yaro jarumi mai haskawa, an zabe shi a cikin gwarazan yara kanana a lambar yabo na Kannywood wanda akayi a watan Janairu. Duk da cewan ya kasance karamin yaro, ya kai matakin tauraro. Shine tauraro a wani sabon fim da aka saki, ‘Khalifa’. Ahmad ya fito tare da Adam Zango a fim din. Jakadan kamfanin madarar Blue Boat, ya nuna bajinta a fina-finan Carbin Kwai, da Akan Idona. Yana da mabiya sama da 57,000 a Instagram.
Asali: Legit.ng