Karfin hali! Tsohuwa da yin fashi

Karfin hali! Tsohuwa da yin fashi

Wata budurwa ta sha da kyar, bayan wata tsohuwa tayi yunkurin yi mata fashi da makami da tsakar rana a ranar Laraba 14 ga watan Disamba a jihar Legas.

Karfin hali! Tsohuwa da yin fashi
Karfin hali! Tsohuwa da yin fashi

Budurwa mai suna Elle ta bada labarin ne a shafin ta na Instagram, inda tace lamarin mai cike da ban mamaki ya faru ne lokacin da ta shiga wani shago don yin siyayyan bikin kirismeti:

KU KARANTA:EFCC su kama Sakataren gwamnatin tarayya idan da gaske suke - Fayose

“Jama’a ku kula da kyau musamman a wannan lokacin na karshen shekara! Na shiga wani katafaren shago a tsibirin Legas da mislain karfe 2:30 na rana, shigana keda wuya sai na lura wata tsohuwa tana bina a baya, duk inda nayi, sai tayi, can sai tace min ‘yarinya ki kula da kudinki sosai fa, kinsan barayi sunyi yawa a Legas’har ma ta bani shawara da in rike wasu daga cikin kudadena a hannu, saboda koda wani ya kwace min jaka, ina da na mota, ni kuwa nayi mata godiya.

“Ban san me ya kai ni ba, sai na ciro kudaden na rike su a hannu, sai tsohuwar nan ta dauko wata karamar leda ta daure min kudaden. Bayan ta daure kudaden sai ta miko min su, na sake yi mata godiya. Ashe matar nan mai siddabaru ce, ina dubawa ledar sai naga tarin jaridu ne kawai a ciki, sai na sa ihu ina kururuwa, nan da nan tsohuwar nan ta ciro kudina ta bani. Don haka jama’a ku kula.”

Ana samun labaran mu a nan da nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel